An sabunta shi a ranar 20 ga Mayu, 2021
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cutar coronavirus a matsayin annoba a duniya a ranar 11 ga watan Maris.
Ana ta samun canje-canje game da yaduwar cutar sannan kasashen duniya na ta sassauta dokar kulle da aka saka, da kuma dokokin hana tafiye-tafiye sannan kuma da sabbin hanyoyin samar da kariya ga wata nau’in cutar Corona da ta bayyana da yadda aka maida hankali wajen ganin ana yi wa mutane rigakafin cutar kamar yadda labarai da rahotanni suka nuna.
‘Yan jarida a fadin duniya na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan mutane game da barkewar annobar coronavirus da kokarin da gwamnatocin kasashen duniya ke yi wajen dakile yaduwar cutar. Duk da cewa kuwa akwai wasu kasashen duniya da ke yi wa ‘yan jarida masu zaman kansu bita da kulle domin hana su dauko labarai da bayanai yadda suke aukuwa kamar yadda CPJ ya tsara.
Hakan na nuna cewa lallai galibin ‘yan jarida za su fuskanci hadarin kamuwa da wannan cuta ta hanyar tafiye-tafiye, tattaunawa ko hira da mutane da kuma wuraren da suka tsinci kan su a lokacin aikin dauko labarai, kamar yadda yake a tattaunawar CPJ da ‘yan jarida. ‘Yan jarida na cin karo da matsi, ana muzanta masu da cin zarafin su a gaba da gaba da a yanar gizo, dama rasa gane inda mutum ya dosa a rayuwa saboda COVID-19, kamar yadda yake kunshe a rahotannin CPJ na kwana-kwanan nan.
Domin zama cikin shiri da sanin abubuwan da ake ciki a duniya game da annobar Corona a duniya da suka hada da shawarwari, ‘Yan jarida da ke aikin dauko labara su maida hanklai wajen bibiyar shafin hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO da kuma cibiyoyin kiwon lafiya dake kusa da su.
Haka kuma za a iya samun sahihan bayanai game da cutar Corona a Cibiyar samar da bayanai kan Coronavirus dake Jami’ar John Hopkins .
Kare kai da kiyaye wa a lokacin dauko Labarai
Dokar hana tafiye-tafiye zuwa kasashen waje na canja wa akai-akai. Hakan na nufin cewa za a iya samun sauye-sauye a yanayin aiki ba tare da an shirya yin hakan ba ko kuma an sanar maka.
Ma’aikatan aikin jarida musamman wadanda aka yi wa rigakafin COVID-19 su kwana da sanin cewa duk da anyi wa mutum rigakafin cutar za su iya yada kwayoyin cutar, kamar yadda cibiyar kula da dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka CDC ta wallafa, sannan kuma shi kan sa allurar rigakafin ya banbanta da yadda yake aiki a kan kwayoyin cutar a jikin mutum, kamar yadda Yale Medicine ya bayyana. A dalilin haka kuwa yake da kyau a ci gaba da kiyaye dokokin COVID-19 wadanda suka hada da tsaya wa nesa da mutane sannan kuma da saka takunkumin fuska a koda yaushe.
Ga ‘Yan jaridan da za suyi aikin dauko labarai a wannan yanayi na annobar COVID-19, ga shawarwari na musamman da hanyoyin kare kai da za a bi kamar haka:
Kafin A Fita Zuwa Aikin Dauko Labarai
- Idan zai yiwu mutum ya yi allurar rigakafin cutar tun da wuri kafin lokacin da mutum zai fita zuwa aiki idan yin hakan babu matsala a wurin sa, musamman idan mutum zai yi aiki ne ko zai yi tafiya zuwa wurin da cutar ta yi tsanani sosai.
● Ya dangana da yadda cutar ta yi tsanani a wurin da kake, yin hira ta wayar tarhon tafi da gidan ka ko ta hanyar yanar gizo sun fi dacewa da mahimmanci akan a hadu gaba-da-gaba da wanda za a yi hira da shi.
● A rahoton Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasar Amurka (CDC), Tsofaffi da wadanda ke fama da wani rashin lafiya mai tsananai kamar ciwon hawan jini da kiba, sun fi zama cikin hadarin kamuwa da kwayoyin cutar matuka. Idan kana daga cikin irin wadannan mutane, kuma da yadda matsayin kamun da cutar ta yi wa mutum abinda ya fi dacewa shine kaurace wa cudanya da mutane. Sannan a yi wa ma’aikata mata masu ciki kyakkyawar tanadi.
● Idan za a zabi ma’aikatan da za su yi akin dauko labaran annobar COVID-19, mahukunta su lura da inda za a tura ma’aikaci don yin aiki domin gudun yiwuwar samun matsalar nuna wariyar launin fata da ake yi wa wasu ‘yan kasashen, kamar yadda aka tsara kuma aka wallafa a jaridar New York Times
● Ana samun sauye-sauye a dokokin hana tafiye-tafiye da saka dokar hana walwala wato kulle ba tare da an sani ba a kasashen duniya. Saboda haka a tattauna irin shiri ko tsari da matakan da ma’aikatar ka ta yi ko ta tsara idan rashin lafiya ya kama ma’aikaci a lokacin da yake aiki, ganin cewa akwai yiwuwar za a iya killace mutum, ko a tilasta wa ma’aikaci ya killace kansa na dole ko kuma ma za a iya zuwa wurin da aka saka dokar hana walwala a dalilin wannan cuta, hakan kuma ya sa dole sai ka wuce wa’adin zaman da kayi niyyar yi a wannan wuri da zaka yi aiki.
Kiyayewa Daga Fadawa Cikin Yanayi Na Fargaba Da Damuwa
● Ka sani ‘Yan jaridan da suka kware a aikin dauko labarai ma za su iya fadawa cikin fargaba a lokacin dauko labaran annobar COVID-19. Kamar yadda cibiyar karo ilmi na Reuters ta jami’ar Oxford ta wallafa Dole shugabanni su rika bibiyar sanin halin da ma’aikatan su ke ciki a wuraren da suke aikin dauko labarai. Sannan su rika basu shawarwari da duk wani taimako da suke bukata idan hakan ya taso.
● Ka maida hankali wajen gujewa fadawa cikin yanayi na fargabar dake tattare da aiki dauko labarai daga wuraren da cutar COVID-19 ta yi tsanani musamman idan wurin da za a yi aiki wuri ne na kula da marasa lafiya ko kuma inda aka hana shiga ko fita ne wato an saka dokar kulle. Za a iya samun bayanai kan yadda ma’aikatan ‘yada labarai da suke aiki a yanayi na fargaba a Cibiyar aikin jarida da kau da fargaba na DART domin samun bayanan yadda za a kare kai, kiyayewa da kauce wa fadawa cikin yanayi na fargaba a lokacin aiki dauko labaran COVID-19. Za a iya samun karin bayani a shafin gaggawa ta CPJ, domin sanin yadda za a kiyaye da sanin yadda dan jarida zai yi aikin dauko labarai a irin wannan yanayi ba tare da ya fada cikin tashin hankali ko fargaba ba.
Kiyaye Kai Daga Kamuwa Da Yada Cuta
Kasashe da dama yanzu na yin gargadi da a rika yin nesa-nesa da juna da hana gwamatsuwar mutane wuri daya. Sai dai kuma wannan doka ya banbanta ga kasashe, ya danganta ne da irin wanda ake yi a kasar da kake. Idan za kayi aikin dauko labarai daga wurare da cutar ta yi tsanani, ka tabbata ka nemi sanin matakan da aka saka domin samun kariya tun da wuri. Idan kaga hankalinka bai kwanta a kai ba ko kuma kana kokwanto, kada ka ziyarci wurare kamar haka:
● Cibiyoyin kiwon lafiya
● Gidajen kula da tsofaffi
● Gidan wanda bashi da lafiya, ko kuma yana da wani ciwo da yake fama da shi.
● Duk ma’aikatar da ake kyautata zaton yaduwar cutar zai yi tsanani kamar masana’antar sarrafa nama, wato mahauta ko kwata.
● Dakunan ajiye gawan wadanda suka rasu, da wurin bizne matattu da duk inda ake mu’amula da gawarwakin mutane.
● Yankunan da aka killace, ko aka hana zirga-zirga a wuraren domin dakile yaduwar cutar.
● Inda yake a cunkushe (Yankunan matalauta). Wato irin unguwanni ko yankuna da yake a gwamutse, irin lunguna da wuraren da ake cunkushe
● Sansanonin ‘yan gudun hijira da gidajen kason da aka samu rahoton bullar cutar COVID-19 a ciki.
Tabbatattun shawarwari don kauce wa kamuwa da cutar sun hada da:
● Ka yi nesa da mutane kamar yadda aka tsara dokar, sai dai kuma dokar yin nesa-nesa din kan banbanta da inda kake, wato yadda mahukunta suka amince ko suka saka za a rika yi ko bi. Sannan ka kiyaye kusantar musamman wadanda ke nuna alamun ciwon yankewar numfashi, tari da atishawa. Haka kuma a rika nesa da musammam tsofaffi a lokacin da ake tattaunawa da su, da kuma wadanda ke da matsaloli na rashin lafiya a baya, makusantan su, ma’aikatan kiwon lafiya da ke aikin kula da masu dauke da COVID-19, ko kuma ma’aikatan da suke wuraren da cutar ta yi tsanani.
● Idan ya kama za ka hira da wani, a yi a waje ne ya fi. Idan kuma dole sai anyi a cikin daki to a bude tagogi domin iska ya rika shiga ta ko ina sannan yan da matukar mahimmanci a yi irin wannan hira ba a tsukakken wuri ba
● Kada ka yi musabahar hannu da kowa sannan a nisanta kai dada runguma ko sumbatar juna.
● Idan za aka yi Magana da mutum ka tsaya a karkace ta gefe maimakon gaba-da-gaba sannan a yi nesa da juna.
● Wanke hannaye a ko da yaushe kuma da kyau na akalla sakan 20 da ruwan dumi da sabulu. Ka tabbata hannayen sun tsantsane kuma sun bushe sosai ta hanya mai kyau. Za a iya samun hanyoyi da yadda za a wanke hannaye da kyau a shafin WHO.
● A yi amfani da man tsaftace hannu idan babu ruwan dumi. Sai dai ayi kokari a wanke hannu da ruwan dumi cikin gaggawa idan aka samu dama. (CDC) ta hori da a rika mafani da man tsaftace hannaye dake dauke da sinadarin Ethanol 60% ko isopropanol 70%.) Kada a sauya wanke hannu da amfani da man tsaftace hannaye a kullum.
● A rika rufe baki da hanci lokacin da ake tari ko atishawa da gefen guiwar hannu. Idan kayi tari ko atishawa a cikin tishu, a gaggauta jefar da shi a kwandon shara, sannan kada a manta a wanke hannaye sosai bayan haka.
● A daina shafar fuska, taba hanci, baki da kunne, da dai sauransu.
● Kada a yi musabaha da hannu, rungume juna ko kuma sumbatar juna. Maimakon haka a rika gaisuwa ta hanyar goga guiwar hannun juna ko kuma kafafuwa.
● Kada a yi amfani da kwanuka, cokula da kofunan shan ruwa da wasu suka yi amfani dasu.
● A rufa kai sosai, sannan idan ana da dogon gashi a nade shi da kyau a rufe kan.
● A cire sarka, zube, agogo kafin a fantsama wurin aiki. Ka sani cewa kwayoyin cutar na iya mannewa ya zauna a jikin abu na tsawon lokaci.
● Idan ana saka tabarau, wato gilas a ido, a rika wanke su da ruwan zafi da sabulu akai akai.
● Idan zai yiwu kada a saka gilashin rufe kwayar ido wato (Contact Lenses) a lokacin da ake aiki saboda gujewa koda a kai ga saka hannu a ido da hakan zai iya sa mutum ya ba kwayoyin cuta damar shiga jikin sa.
● A maida hankali matuka kan irin kayan da za a saka, wasu kayan za a iya goge su kai tsaye, wasu kuma ba haka ba. Idan za a cire kayan da aka saka lokacin da aka fita aiki, a tabbata an cire su cikin natsuwa da kula matuka. Sannan a wanke kayan da ruwa zafi da kuma sabulu sosai.
● Idan zai yiwu kada a rika mu’amula da kudi a lokacin da ake aikin dauko labarai. Sannan a rika goge katin ciro kudi wato ATM, da jakar ajiyar kudi a aljihu a kai-akai. Kuma ma a daina yawan saka hannu a aljihu.
● Idan zai yiwu a nisanta kai daga shiga ko amfani da motocin haya musamman a lokuttan da mutane ke gaggawar zuwa wuraren aiki da harkokin yau da kullum. Sannan kuma ka tabbata kana tafe da man tsaftace hannu tare da kai.
● Idan kuma a motar ka kake a ciki, a kula sosai kada wani mai dauke da kwayoyin cutar ya gogi wani dake cikin motar, a bude tagogi domin iska ya rika shiga yana fita sannan kuma idan da hali ma a yi amfani da takunkumin fuska.
● A rika daukan hutu lokaci-lokaci, domin idan aka gaji da yawa za a rika yawan yin kuskure da mantuwa game da kiyaye kiwon lafiya. Saboda a dalilin yanayin irin aikin da ake yi mutane za su yi dogon tafiya wajen zuwa da dawowa daga wuraren ayyukan su.
Kayan Aikin Na Samar Da Kariya Ga Kiwon Lafiya (PPE)
Ya danganta da irin aikin da mutum zai yi, ma’aikatan jarida na bukatar su rika saka wasu kayayyaki na kare lafiyar su a lokacin aikin dauko labarai. Wadannan kaya kuwa sun hada da safar hannu, takunkumin fuska, safa da takalman aiki. Wadannan kayan na bukatar a maida hankali matuka wajen kula da tsaftar su da yadda za a tsaftace su domin za su iya zama hadari idan ba ayi taka tsantsan ba. Dole sai an maida hankali. Za a samu cikakken bayani game da samun kula da kariya a shafin CDC a yanar gizo.
Akwai yiwuwar a gurbata kayan da za a yi amfani da su (PPE) da kwayoyin cuta a wajen sakawa da lokacin cire kayan. Idan kana shakku ka nemi shawarar kwararru su yi maka bayani, kafin a fita zuwa aiki.
A sani cewa a kasashe da dama, ire-iren wadannan kaya da ake sakawa na samun kariya kan yi karanci sosai saboda haka amfani dasu kan iya sa ayi fama da karancin su.
● A saka kaya kare jiki da yayi daidai da jiki. Saboda wanda ya yi kadan kan iya yagewa, idan kuma ya yayi yawa zai iya yana jan kasa ko kuma kama hannayen kofa su yage a lokacin da ake cikin aiki.
● Ayi amfani da kayan samun kariya masu nagarta da aminci. A kula da kayan da basu da aminci. A bi nan domin samun kaya masu aminci da nagarta
● A saka safar hannu lokacin aiki ko kuma a lokacin da aka ziyarci mara lafiya. Idan so samu ne ma a sake guda biyu a hannu.
● Idan za a yi aiki a wuraren da annobar ta yi tsanani yana da matukar mahimmanci a tafi da karin kayan sawa kamar rigar kariya da takunkumin fuska da safar hannu da dai sauran kayan kare jiki da za a bukata.
● Idan za a saka kayan kariya duk jiki ne a tabbata an yi amfani da ban daki kafin a saka saboda kaucewa lalurar haka zai iya tasowa.
● Sannan kuma yana da matukar mahimmanci a samu kwararre ya adana kayan aiki na kariya da za a fita da su domin ko anan ma akan iya gurbata su da kwayoyin cuta.
● Ma’aikaci na bukatar saka takaman da ruwa baya ratsa su ko kuma takalman aiki da ake rabuwa da su bayan an yi amfani da su. Sannan kuma a tabbata an wanke su tsaf bayan an gama amfani da su kafin a bar wurin aiki. Idan na yar wa ne a tabbata an jefar da su yadda ya kamata kafin a bar wurin.
● A tabbata an saka kuma an cire kayan kariya a karkashin kulawar kwararru. Saboda zai iya yiwuwa wannan lokaci ne za su iya kwasar kwayoyin cuta. Wannan bidiyo game da yadda za a saka da cire kaya daga CDC zai taimaka matuka sai dai kada a dogara da shi aki zuwa a koyi yadda ake saka kayan da cirewa kamar yadda kwararru suka koyar.
● Ka da a yi amfani da safar hannu wanda sau daya ya kamata a yi amfani da shi a sake saka shi sau biyu, ko kuma rigar aiki dake rufe jiki ko takalman aiki (PPE) . Idan akwai abin da za a iya sake amfani dasu, tabbas sai kwararru sun tsaftace su da sinadarin kashe kwayoyin cuta. Sannan ka tabbata an jefar da duk wani abinda ba za a sake amfani da shi ba kafin a bar wurin.
Takunkumin Fuska
Saka takunkumin fuska na dada zama dole yi musamman ga ma’aikatan jarida a lokacin da suke aikin dako labarai a cikin jama’a ko a wuararen da aka kebe da kuma wuraren da akwai annobar ta yi tsanani.
Ya zama dole a maida hankali kuma a sani cewa akwai yiwuwar iya kamuwa da kwayoyin cutar COVID-19 ta hanyar shaka a iska musamman a wuraren da suke kebabbu wato kamar killatacen wuraren da ake samun karancin gudanar iska. Wurare irin haka suna da hadarin gaske wajen iya kamuwa da kwayoyin cutar wanda kuma hakan zai saka ka cikin hadari matuka.
Sai dai kuma a tabbata an saka takunkumin da yadda ya kamata domin rashin haka zai iya jefa mutum cikin hadarin kamuwa da cutar.
A wani rahoton binciken Lancet, kwayoyin cutar kan iya zama a jikin takunkumin har na tsawon kwanaki bakwai bayan anyi amfani da shi, ko kuma taba fuska a lokacin da aka saka shi kan zama hadari ga mutum.
A dalilin haka, cire takunkumin, ko kuma amfani da wanda akayi amfani dashi a baya zai iya zama hadari.
Idan za a saka takunkumin fuska a tabbata an bi wadannan ka’idoji dake tafe:
● Idan mutum zai yi aikin dauko kabarai a killataccen wuri ko kuma inda hadarin kamuwa da cutar ya yi tsananin gaske, abin da yafi dacewa shine a sake takunkumi fuska kirar N95 ko kuma (FFP2/FFP3) maimakon wanda likitoci ke sakawa idan za suyi aikin fida a asibiti.
● Sannan kuma a tabbata ya rufe ko-ina a fuska tun daga hanci da gefen kumatu, kuma a tottoshe kafofin gefen kumatu.
* A aske duka gashin fuska ko kuma a rage shi matuka saboda takunkumin ya zauna da kyau a fuskar mutum ba tare da an samu wani kafa da kwayar cutar za ta shiga baki ko hancin mutum ba.
● Kada a rika taba shi wannan takunkumi idan aka saka kuma ida za a cire ayi amfani da igiyan sabulewa. Kada a kuskura a taba fuskar takunkumin. A gaggauta wanke hannu idan aka taba takunkumin.
● A rika wanke hannu a koda yaushe da ruwan dumi da sabulu ko kuma da man tsaftace hannaye dake kasha kwayoyin cuta mai kunshe da sinadarin ethanol akalla kashi 60% ko 70% na isopropanol bayan an cire takunkumin fuska.
● A gaggauta canja takunkumin fuska da wani idan ya dade a jiki da sabo kuma mai tsafta.
● Kada a sake amfani da takunkumin da aka yi mafani dashi a baya, sannan idan za a jefar a saka shi cikin rufaffen jakar tara bola.
● A tuna cewa shi saka takunkumin fuska daya daga cikin hanyoyin kare kai ne, dole sai ana kuma wanke hannaye da ruwan dumi da sabulu sannan a daina taba fuska da ya hada da idanu, baki, kunnuwa da hanci.
● Auduga da takunkumin kyalle basu inganta a yi amfani da su ba kwata-kwata.
● Wani abu kuma da ya kamata ka sani shine shi takunkumin fuska kan iya yin karanci ko kuma su yi tsadar gaske, sai dai ya danganta ne da inda kake aiki.
Tsaftace Kayan Aiki
A kwai tabbacin cewa za a iya yada cutar COVID-19 ta hanyar kayan aikin da aka gurbata su da kwayoyin cuta. Dole a maida hankali wajen tsaftace su yadda ya kamata domin gudun kada a kamu da cutar kamar haka:
● A rika amfani da na’aurar daukar sauti mai tsawo wanda za a zuro shi daga can nesa. Sannan kuma idan har za a yi amfani da na’urar daukan sauti wanda sai dole an makala a jikin mutum, a tabbata an bi dokokin samun kariya da kiyaye wa daga kamuwa da kwayoyin cuta.
● A rika rufe na’urar daukan sauti da rigarta sannan a goge da sinadarin kashe cuta idan aka gama aiki. A nemi sani da karin bayani game da yadda ake cire rigar na’urar domin kada a yada cuta.
● A yi amfanin da na’urar sauraren sauti da ake saka wa a kunne masu sauki. Wadanda idan aka gama amfani da su za a iya rabuwa da su. Amma wadanda za a ci gaba da amfani dasu a tabbata an tsaftace su da kyau bayan an kammala aiki.
● Ayi amfani da na’urar daukan hoto daga can nesa maimakon wanda yake dauka daga kusa. Hakan zai sa ayi nesa da wurin da ake fargaban kusanta domin kare kai.
● Idan zai yiwu ayi amfani kayan aikin tafi da gidan ka, ba wadanda sai anyi amfani da igiyoyin ko jone-jone ba.
● A kula da yadda za a adana kayan aiki. Kada a jibge su a kasa. A maida su cikin akwatunan kayan aiki da jakkuna. Yana da kyau a yi amfani da akwatuna masu nagarta wadanda za a iya gogesu da man kasha kwayoyin cuta, a tsaftacesu bayan aiki.
● Idan zai yiwu a rika nade kayan aiki da murfin roba. Hakan zai rage sa kaya su kwashi kwayoyin cuta ko su gurbata da kwayoyin cuta. Kuma idan an gama aiki za a iya goge su da kyau ya fita.
● A tanadi batir din aiki guda biyu. Saboda a wajen kokarin cajin daya zai iya gurbata shi da kwayoyin cutar da za su iya shiga jikin mutum.
● A gaggauta goggoge kayan aiki da zaran an kammala aiki da sinadarin kashe kwayoyin cuta kamar Meliseptol, sannan a tabbata an goge da tsaftace wayoyin hannu, wayoyin wuta da kayan aiki, na’urar daukan hoto, da na bidiyo wato kamarori, Komfutoci da ababen adana da sauran su.
● Sannan kuma kafin a maida su wuraren da ake ajiyar su, a goggoge su, kuma a sanar wa masu kula da ajiyan wadannan kaya da kula da su a wuraren ajiyan domin sun san yadda za su rika kula da kayan aiki da tsaftace su. A tabbata ba a ajiya kayan aiki barkate ba tare da an shigar su cikin jadawalin kayan da aka dawo da su ba sannan a tabbata ana kula da tsaftace su.
● Idan baka da sinadarin tsaftace kayan aiki. Ka sani cewa zaka iya baza su a rana na dan wani lokaci. Hakan na kashe cuta da ya manne a jikin kayan aiki. Za ayi hakanne idan babu yadda za ayi domin yin hakan zai iya illata wasu kayan aikin.
● Idan za a yi amfani da mota ne a tabbata an tsaftace cikin motan da kyau musamman bayan an dawo daga wurin aiki. A samu wadanda suka kware wajen yin irin wannan aiki a basu su yi, za a goge hannun kofofin mota, sitiyari, maduban hangen baya, radiyo, bel din kujeru, saman cikin mota da duk wani abu makamancin haka.
Tsaftace Na’urorin Dake Amfani Da Wutar Lantarki
A nan zamu bada shawarwarin da ya kamata abi wajen tsaftace kayan aiki da suka shafi wutan lantarki. Na farko dai ka tabbata ka karanta takardar da ke kunshe da na’urar wanda da ya zo da shi a kwali tun daga kamfani.
● Ka tabbata ka cire duk wani yawa dake makale da wurin wuta daga na’urar ka.
● A kauda duk wani abu na ruwa kusa da kayan aiki, wato na’urar ka. Kamar su man tsaftace wuri. Barin su su taba wannan kayan aiki zai iya lalata su.
● Kada ka fesa koma maenene akan na’urar ka
● Ayi amfani da kyalle masu laushi sannan masu tsafta wajen tsaftace kayan ka.
● Adan yayyafa wa wannan kyalle ruwa amma ba a jika shi ba sannan a goga masa sabulu kadan.
● Daga nan sai a rika goge shi daga sama har kasa ana yi ana dawowa har ya fita.
● A kula kada ruwa ya shika cikin wuraren da ke bude a, kamar soket na wuta, da wuri tafin na komfuta da na’urar sauraren Magana wato Earphone.
● A goge na’urori da kyallen da yake a bushe bayan haka.
● Wasu daga cikin kamfanonin kere-kere kan so ayi amfani da kyallen da ke dauke da akalla kashi 70% na sinadarin Isopropyl.
● Idan kana so ka tsaftace kayan aikin ka wato na’urorin ka, ka nemi bayanai daga kamfanin da suka yi wadannan na’urori domin akan samu matsala idan ba a fara bi daga wurin su ba anga irin sharuddan da suka saka akai ba.
Za a iya samun karin bayani a nan
Kariya Daga Muzantawa Daga Yanar Gizo
● Dole ne ‘yan jarida su kwana da shirin cewa za a rika cakalar su da muzanta musu kan labarai da rahotannin da za su rika yi kan annobar cutar COVID-19. Tsangwama zai iya zuwa daga wadanda basu ra’ayin allurer rigakafin annobar ko kuma wadanda bas u amince da a rika saka takunkumin fuska ba. Ka bi shafin CPJ domin samun bayanan yadda za ka kare kan ka, da yadda za ka kiyaye daga fadawa hannun ire-iren wadannan mutane da za su rika muzanta maka.
● Gwamnatoci da kamfanonin fasaha na amfani da fasahar zamani don bin diddigin yadda cutar COVID-19 ke yaduwa a duniya. Kamfanin NSO Group da ta kirkiro da Pegasus manhaja ko na’urar da ake iya bin diddigin ‘yan jarida da halin da suke ciki idan aka afka musu tsangwama ko makamancin haka. Kamar yadda Citizen Lab ya bayyana. Kungiyoyin rajin kare hakkin mutane sun afka cikin fargaba da nazarin yadda za ayi amfani da wannan fasaha ko na’ura wajen bin diddigin ayyukan ‘yan jarida. Haka ita ma kungiyar bin diddigi ta (Transparency International) na bibiyar ayyuka irin wadannan miyagu a shafinta dake yanar gizo.
● A kwai miyagu da ke amfani da wannan lokaci da ake kaikomo kan da annobar ta hanyar aika wa mutane ko kamfanoni sakonni karya musamman wanda ya shafi rigakafin annobar wanda shine ake amfani da kamar yadda rahotanni suka nuna. Kuma ka yi taka tsantsan da irin shafukan da zaka rika bi a yanar gizo wajen nemo ko samun bayanai kan cutar COVID-19 da allurar rigakafin cutar sannan a dalilin haka su aika da wasu muggan kwayoyin cuta da aka kirkira da zasu iya illata na’urar ka sannan su rika aikawa da bayanan ka na sirri a boye, kamar yadda cibiyar Electronic Frontier Foundation ta wallafa. Sannan kuma a kula, a kuma maida hankali da shafukan da za a rika bude domin samun labaran annobar Covid-19 musamman a shafukan sada zumunta wato soshiyal midiya ko kuma sakonni na kai tsaye wanda dag aka latsa su don shiga shafukan za saka wa na’urar Komfutar ka wata kwayar cuta, ta birkice.
● A yi takatsantsan da rahotannin karya da wasu hukumomin gwamnati ke biya a saka kamar yadda aka ruwaito a jaridar The Guardian, da kuma rahotannin da basu tabbata ba kamar yadda hukumar WHO ta yi gargadi kan haka kuma BBC ita ma ta fitar da bayanai kan haka. Akwai wani kundin bayanai game da haka mai suna A Myth buster guide a shafin WHO.
● Ka yi bincike da nazarin sanin tsaro na yanar gizo sannan ka san wani shafi kake ziyarta kuma ka ke tura sako da samun bayanai, sannan kuma da sanin matsayin tsaron shafin kafin ka yi hulda da su. Domin mutane da dama suna zaman gida dole, hakan zai ba masu satar bayanai damar cin karen su ba babbaka.
● A yi takatsantsan wajen dauko labarai daga kasashen da gwamnatocin su ke da tsauri wato gwamnatin kama karya wanda za ta rika bibiyar yadda ake dauko wa da yada labarai game da annobar cutar COVID-19. Wasu gwamnatocin za su so su boye ainihin bayanai game da cutar ko kuma sai sun tantance gidajen jaridun da za su rika dauko labarai a kasashen su kamar yadda CPJ ta bayyana a shafinta.
Laifuka da Tsaron Kai A Lokacin Aiki
● Idan har za ka yi tafiya aiki kasashen waje ka duba nan. Ka tabbata ka yi bincike mai zurfi kan yanayin abubuwa a inda zaka tafi aiki. Sanin cewa an rika samun tashin hankali da zanga-zanga a kasashen duniya tun da annobar ta bayyana.
Yan jarida da dama sun ba da rahoton cewa an muzguna musa ta kai tsaye wasu ma har hari an kai musu, saboda haka dan jarida ya tabbata bai yi wasa da tsaro da lafiyar sa ba.
● ‘Yan jarida su kiyaye matuka idan aiki ya kai su kauyuka ko karkara, domin wasu basu saba da baki ba, kuma za su iya yi maka ganin kai ma kana dauke da cutar.
● A kuma maida hankali wajen kiyayewa da fushin ‘yan sanda lokacin aiki musamman a lokacin da suke kokarin tabbatar da dokar zaman kulle da aka saka saboda annobar COVID-19, sannan kuma da sanin cewa akwai yiwuwar za a iya afka maka a ci zarafin ka , sannan kuma zai iya kaiwa ga yin amfani da barkonon tsohuwa.
● Lallai dole dan jaridan dake aiki a kasashen da ake mulkin kama-karya ya zamo cewa a kullum yana zaune ne cikin shirin yi masa barazanar ko a kama shi a daure ko a cafke shi a lokacin da yake aikin dauko labaran cutar COVID-19 kamar yadda CPJ ta bayyana.
Aikin Dauko Labarai Daga Wata Kasar
A dalilin dokar hana tafiye-tafiye da kasashen duniya suka saka, yanzu tafiya zuwa wata kasa baya samuwa cikin sauki kamar a baya. Idan har tafiya zuwa wata kasa ya kama ka, ga matakan da zaka bi:
● Ka yi binciken sabbin dokoki game da shige da ficen kasashen da zaka domin akan samu canji kwatsam ba tare da an sanar da haka ba.
● Ka sani cewa dokar hana zirga-zirga kan banbanta daga kasa zuwa kasa. Kuma za a ci gaba da samun irin wadannan canje-canje ba tare da mahukunta sun yi sanarwa akan haka ba. Saboda haka dole ka rika bibiyan labaran cikin gida domin sanin sabbin dokoki da aka saka a inda kake.
* Za a iya killace ka ba tare da an sanar maka da haka ba da zaran ka dawo daga aikin dauko labarai. Hakan kuma ya nasaba ne da kasar da ka dawo aiki daga ko kuma inda ka nufa aiki.
● Ka nemi sanin matsayin kiwon lafiya a kasashen da zaka je aiki. Ma’aikatan kiwon lafiya za su iya yin shiga yajin aiki a kowani lokaci ba tare da an sanar da haka ba.
● Samun kayan kariya zai iya yin karanci ko kuma a rasa su kwata-kwata. Ka tabbata ka yi bincike mai zurfi game da yadda zaka mallaki naka ko kuma mafi sauki ka tanadi naka kafin ka fita zuwa aiki.
● Idan zai yiwu ka yi allurer rigakafin cutar ka fin ka fantsama inda zaka tafi aiki Ka tabbata duka rigakafin cututtukan da ya kamata ayi su a duk an yi su a cikin lokaci.
● Ka duba dokokin Inshorar tafiyar ka. Ganin cewa samun wata takarda da zai wanke ka daga cutar COVID-19 zai yi wuyan gaske. Ka sani cewa gwamnatocin kasashe kan bada shawarwari game da tafiye-tafiye da gargadi game da tafiya zuwa kasashen duniya.
● Ka rika duba bayanai game da taron da zaka halarta, saboda kasashe da dama sun hana taron mutane ko kuma taron da ya wuce wani kayyadadden adadin mutane.
● An daddatse iyakokin kasashe a fadin duniya. Wadanda aka bude ma za a iya dates su kuma, saboda haka ya kamata ka tsara irin haka cikin shirin ka na ko ta kwana.
● Kada ka kuskura ka yi tafiya idan baka da lafiya. Kusan duka tashoshin jiragen saman kasashen duniya sun saka tsauraran matakan gwajin lafiyar matafiya.
● Saboda matsalolin karayar arziki da wasu kamfanonin jirage suka afka ciki, kamar yadda yake kunshe a cikin wani sabon rahoto. Saboda haka idan zaka sayi tikiti ka siya wanda za a iya biyan ka kudin ka idan a ka samu matsala.
● Ka duba matsayi ko hanyar samun bizar kasar da zaka tafi domin kasashe da dama sun dakatar da bada biza.
● Ka tabbata ka duba matsayin kasar da zaka je game da takardun shaidar lafiyar ka, ko kila sai ka nuna shaidar baka dauke da cutar COVID-19 kafin a baka damar shiga kasar.
● Ka tabbata ka samu isasshen lokaci a tashoshin jirgen sama domin gwaje-gwaje da za a rika yi da ya hada da na lafiyar ka da na gwajin zafin jikin ka a wurare a filin jirgin. Haka kuma ma a tashoshin jiragen kasa, ruwa da tashoshin shiga manyan motocin haya.
Bayan An Kammala Aiki
● Ka rika duba lafiyar ka akai akai domin gano ko akwai alamun kamuwa da wata cuta
● A dalilin aikin da ka yi bayan kadawo zai iya yiwuwa dole sai ka killace kanka musamman idan ka dawo daga kasar da annobar ta yi tsananin gaske. Ka duba yadda dokokin kasar ka suke domin fahimtar yadda za aka tunkari abin.
● A maida hankali wajen sani da sa ido kan sabbin dokoki ko matakai da bayanai da da za a rika fitar wa game da cutra COVID -19, da kuma bayanai game da killace kai da garkame mutum a kasar ka ta asali da kuma kasar da tafi aiki.
● Yana da matukar mahimmanci ka mallaki jadawalin sunayen wuraren da ka ziyarta, sunaye da yawan mutanen da ka yi mu’amula da su a tsakanin kwanaki 14 bayan ka dawo daga tafiya. Hakan zai taimaka matuka idan ana neman wadanda ka yi mua’amula da su a lokacin da aka fara ganin alamun rashin lafiya a jikin ka.
—Idan Ka Nuna Alamun Rashin Lafiya
● Idan ka fara jin alamun rashin lafiya irin ta COVID-19 komai kankantarshi Ka nemi shugabannin ma’aikatarka su san halin da kake ciki domin su nema maka motar da zai kai ka gida maimakon ka yi gaban kanka ka fada motar haya kawai ka yi tafiyar ka.
● Ka tabbata ka bi shawarwarin da hukumar lafiya ta duniya, WHO, CDC da ma’aikatar kiwon lafiya suke bayarwa domin kare kanka da na al’umma gaba daya.
● Kada ka fita daga gidan ka na tsawon kwanaki 7 daga lokacin da ka fara jin alamun rashin lafiya. ( Koda yaka ainihin lokacin da za ka iya fita ko yin mu’amula ya danganta da yadda gwamnatin kasar ka ta tsara ne bias shawarwarin da za a baka.) Yin haka zai taimaka wajen kare al’umman da kuke zaune tare a lokacin da ka kamu da kwayoyin cutar.
● Ka tsara wa kanka yadda zaka yi zama a killace. Ka nemi taimakon wadanda kuke tare. Abokanan aikan ne, abokai da ‘yan uwanka su taimaka maka da abubuwan da kake bukata, su ajiye maka a kofar dakin da kake. Daga baya kai ka fito ka dauka
● Ka tabbata ka bi dokokin yin nesa da mutane kamar yadda mahukuntan kasarka suka ayyana ko tsara.
Kwamitin Kare ‘Yan jarida CPJ ya samar wa ‘Yan jarida da dakunan ‘yada labarai muhimman bayanai kan yadda za su rika kiyaye kan su a duk halin da suka tsinci kansu na aiki, kai tsaye ne, ta yanar gizo ne da kuma yadda zaka inganta tunanin ka da kauce wa fadawa cikin fargaba da rudani da fadawa cikin damuwa da yadda za a kiyaye, har a lokacin da ka tsinci kanka wajen dauko labarai lokuttan rashin zaman lafiya da lokuttan zabe.
[ Sakon Mawallafi: An wallafa wannan shawarwari a karon farko ranar 10 ga watan Fabrairu, 2010, sannan kuma ana ingantashi akai-akai da sabbin bayanai. Ranar da aka saka a saman wannan rubutu, shine sabon bugu da aka yi na karshe.]