‘Yan jaridar kasar Mexico sanye da kayan kariya a yanayi na annobar COVID-19, wajen aikin dauko labaran zanga-zangar ma’aikatan sashen gudanarwa na Babban Asibitin Balbuena dake cikin garin Mexico ranar 16 ga Afrilu, 2020. (AFP/Pedro Pardo)

Shawarwarin samun Kariya daga Kwamitin Kare ‘Yan jarida, CPJ: Aikin dauko Labaran annobar Coronavirus

An sabunta shi a ranar 14 ga Agusta, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cutar coronavirus a matsayin annoba a duniya a ranar 11 ga watan Maris. 

Kasashe da dama na samun raguwar wadanda ke kamuwa da cutar a kullum da hakan yasa kasashe na sassauta dokar kulle da suka saka, kamar yadda Guardian ta ruwaito

‘Yan jarida a fadin duniya na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa mutane kai game da barkewar annobar coronavirus da kokarin da gwamnatocin kasashen duniya ke yi wajen dakile yaduwar cutar. Duk da cewa kuwa akwai wasu kasashen duniya da ke yi wa ‘yan jarida masu zaman kansu bita da kulle domin hana su dauko labarai da bayanai yadda suke aukuwa kamar yadda CPJ ya tsara.

Hakan na nuna cewa lallai galibin ‘yan jarida za su fuskanci hadarin kamuwa da wannan cuta ta hanyar tafiye-tafiye, tattaunawa ko hira da mutane da kuma wuraren da suka tsinci kan su a lokacin aikin dauko labarai, kamar yadda yake a tattaunawar CPJ tare da ‘yan jarida. ‘Yan jarida na cin karo da matsi, ana muzanta su da cin zarafin su a gaba da gaba har a yanar gizo, dama rasa fasaslin rayuwar su a dalilin COVID-19, kamar yadda yake kunshe a rahotannin CPJ na kwana-kwanan nan.

A dalilin yadda wannan matsala za ta ci gaba da bayyana kuma sabbin bayanai za su rika fitowa, yaduwar annobar da shawarwari za su yi ta bayyana daga mahukunta. Domin sanin abubuwan dake faruwa kai tsaye na sabbin shawarwari, dokoki, ya kamata ‘yan jaridan da suke aikin dauko labaran annobar su rika neman bayanai daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, da ma’aikata da cibiyoyin kiwon lafiya dake kusa da su.

Cibiyar samar da bayanai na Jami’ar John Hopkins na bada sahihan alkalumma domin sanin yadda annobar ke yaduwa da halin da kasashe ke ciki a duniya.

Kare Kai da Kiyaye wa a lokacin gwagwarmayar dauko Labarai

Dokar hana tafiye-tafiye zuwa kasashen waje na nan daram kuma yana canja wa akai-akai. 

Aikin dauko labarai zai canja ko kuma ma a soke su kwata-kwata ba tare da an shirya yin haka ba ko kuma an sanar da haka ba, saboda yadda matsalolin za su cigaba da dabaibaye duniya da neman fin karfin kasashe. 

Ga ‘Yan jaridan da za suyi aikin dauko labarai a wannan yanayi na annobar COVID-19, ga shawarwari na musamman da hanyoyin kare kai da za a bi kamar haka:  

Kafin A Fita Zuwa Aikin Dauko Labarai

● Domin kiyaye afkawa cikin hadari, tattaunawa ta wayar tarho ko ta yanar gizo ya fi dacewa maimakon a hadu gaba-da-gaba da wanda za a tattauna da shi. 

● A rahoton Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasar Amurka (CDC), Tsofaffi da wadanda ke fama da wani rashin lafiya mai tsananai kamar ciwon hawan jini da matsannancin kiba, sun fi zama cikin hadarin kamuwa da kwayoyin cutar matuka. Idan kana daga cikin irin wadannan mutane, ka kaurace wa cudanya da mutane. Sannan a yi wa ma’aikata mata masu ciki kyakkyawar tanadi.

● Idan za a zabi ma’aikatan da za su yi akin dauko labaran annobar COVID-19, mahukunta su lura da inda za a tura ma’aikaci domin gudun matsalar nuna wariyar launin fata da ake yi wa wasu ‘yan kasashen, kamar yadda Cibiyar NHK World ta wallafa 

● A wasu kasashen da suka sassauta dokar hana walwala, tuni sun sake saka wa kuma kamar yadda Forbes ta wallafa. Saboda haka a tattauna wani irin shiri da matakai ne ma’aikatar ka ta tsara ko da ya rashin lafiya ya kama ma’aikaci a lokacin da yake aiki, ganin cewa akwai yiwuwar a iya tsare mutum, ko kuma a killace mutum, ko  a tilasta ma’aikaci killace kansa na dole ko kuma ma a iya fadawa wuraren da aka saka dokar kulle a dalilin wannan cuta.

Kiyayewa Daga Fadawa Cikin Yanayi Na Fargaba Da Damuwa 

● Ka sani ‘Yan jaridan da suka kware a aikin dauko labarai ma za su iya afkawa cikin fargaba  a lokacin dauko labaran annobar COVID-19. Kamar yadda cibiyar karo ilmi na Reuters ta jami’ar Oxford ta wallafa Dole shugabanni su rika bibiyar sanin halin da ma’aikatan su ke ciki a wuraren da suke aikin dauko labarai. Sannan su rika basu shawarwari da duk wani taimako da suke bukata idan hakan ya taso.

● ‘Yan uwa da abokan arziki za su shiga damuwa idan suka kaji wani nasu zai je aikin dauko labaran annobar cutar COVID-19. Ka zauna dasu ku tattauna ka ji damuwar su da fargabar su sannan da abinda ke tada musu hankali. Idan zai yiwu ka samu lokaci su zauna da shugabannin ma’aikatar ka da ma’aikatan kiwon lafiyar ma’aikatar domin su wayar musu da kai su kuma kwantar musu da hankali.

● ‘Yan jarida sun shaida wa CPJ cewa  a lokutta da yawa ‘yan uwa da iyaye kan nuna rashin jin dadin su da fadawa cikin fargaba idan nasu na aikin dauko labarai kan COVID-19. Irin haka kan sa dan jarida yaji abin ya fita masa a rai, guiwowinsa su yi sanyi game da aikin.

● Ka maida hankali wajen gujewa fadawa cikin yanayi na fargabar dake tattare da dauko labarai daga wuraren da  cutar COVID-19 ta yi tsanani musamman idan wurin da za a yi aiki wuri ne na kula da marasa lafiya ko kuma inda aka hana shiga ko fita ne. Za a iya samun bayanai kan yadda ma’aikatan ‘yada labarai da suke aiki a yanayi na fargaba  a Cibiyar aikin jarida da kau da fargaba na DART domin samun bayanan yadda za a kare kai, kiyayewa da kauce wa fadawa cikin yanayi na fargaba a lokacin aiki dauko labaran COVID-19. Za a iya samun karin bayani a shafin gaggawa ta CPJ, domin sanin yadda za a kiyaye da sanin yadda dan dan jarida zai yia akin dauko labarai a irin wannan yanayi ba tare da ya samu tashin hankali ko fadawa cikin fargaba ba.

Kiyaye Kai Daga Kamawa Da Yada Cuta

Kasashe da dama yanzu na yin gargadi da a rika yin nesa-nesa da juna da hana gwamatsuwar mutane wuri daya. Sai dai kuma wannan doka ya banbanta ga kasashe, ya danganta ne da irin wanda ake yi a kasar da kake, Kamar yadda Reuters ya wallafa. Idan za kayi aikin dauko labarai daga wurare da cutar ta yi tsanani, ka tabbata ka nemi sanin matakan da aka saka domin samun kariya tun da wuri. Idan kaga hankalinka bai kwanta a kai ba ko kuma kana kokwanto, kada ka ziyarci wurare kamar haka: 

 ● Cibiyoyin kiwon lafiya

 ● Gidajen kula da tsofaffi

● Gidan wanda bashi da lafiya, ko kuma yana da wani ciwo da yake fama da shi ko kuma mace mai ciki. 

● Masana’antar da aka tabbatar cutar ta yi tsanani kamar masana’antar sarrafa nama, wato mahauta ko kwata.

● Dakunan ajiye gawan wadanda suka rasu, da wurin bizne matattu da duk inda ake mu’amula da gawan mutane.

● Yankunan da aka killace, ko aka hana zirga-zirga a wuraren domin dakile yaduwar cutar.

● Inda yake a cunkushe (Yankunan matalauta). Wato irin unguwanni ko yankuna da yake a gwamutse ake babu masaka tsinke.

● Sansanonin ‘yan gudun hijira

● Gidajen Kason da aka samu bullar cutar COVID-19 a ciki.

Muhimman shawarwari don gujewa kamuwa da cutar sun hada da:  

● Ka yi nesa da mutane kamar yadda dokar yin nesa-nesa ya ke, sai dai kuma dokar yin nesa-nesa din kan banbanta da inda kake, wato yadda mahukunta suka amince ko suka saka za a rika yi ko bi . Sannan ka kiyaye musamman ga wadanda ke nuna alamun ciwon yankewar numfashi, tari da atishawa. Haka kuma a rika nesa da musammam tsofaffi a lokacin da ake tattaunawa da su, da kuma wadanda ke da matsaloli na rashin lafiya a baya, makusantan su, ma’aikatan kiwon lafiya da ke aikin kula da masu dauke da COVID-19, ko kuma ma’aikatan da suke wuraren da cutar ta yi tsanani.

● Idan ya kama za ka tattauna da wani, a yi a waje ne ya fi. Idan kuma dole sai anyi a cikin daki to a bude tagogi domin iska ya rika shiga. A rika kaucewa yin haka a kananan dakunan da babu sarari sosai.

● Kada ka yi musabahar hannu da kowa, banda runguma ko sumbatar juna.

● Idan za aka yi Magana da mutum ka tsaya a karkace ta gefe maimakon gaba-da-gaba sannan a yi nesa da juna.

●  Wanke hannaye a ko da yaushe kuma da kyau na akalla sakan 20 da ruwan dumi da sabulu. Ka tabbata hannayen sun tsantsane kuma sun bushe sosai ta hanya mai kyau. Za a iya samun hanyoyi da yadda za a wanke hannaye da kyau a shafin WHO.

● A yi amfani da man tsaftace hannu idan babu ruwan dumi. Sai dai ayi kokari a wanke hannu da ruwan dumi cikin gaggawa idan aka samu dama. (CDC) ta hori da a rika mafani da man tsaftace hannaye dake dauke  da sinadarin Ethanol 60% ko isopropanol 70%.) Kada a sauya wanke hannu da amfani da man tsaftace hannaye a kullum.

● A rika rufe baki da hanci lokacin da ake tari ko atishawa da gefen guiwar hannu. Idan kayi tari ko atishawa a cikin tishu, a gaggauta jefar da shi a kwandon shara, sannan kada a manta a wanke hannaye sosai bayan haka. 

● A daina shafar fuska, taba hanci, baki da kunne, da dai sauransu, kamar yadda BBC ta wallafa ashafin ta.

● Kada a yi musabaha da hannu, rungume juna ko kuma sumbatar juna. Maimakon haka a rika gaisuwa ta hanyar goga guiwar hannun juna ko kuma kafafuwa.

● Kada a yi amfani da kwanuka, cokula da kofunan shan ruwa da wasu suka yi amfani dasu.

● A rufa kai sosai, sannan idan ana da dogon gashi a nade shi da kyau  a rufe kan.

● A cire sarka, zube, agogo kafin a fantsama wurin aiki. Ka sani cewa kwayoyin cutar na iya mannewa da zama a jikin abu na tsawon lokaci.

● Idan ana saka tabarau, wato gilas a ido, a rika wanke su da ruwan zafi da sabulu akai akai.

● Idan zai yiwu kada a saka gilashin rufe gwayar ido wato (Contact Lenses) a lokacin da ake aiki saboda gujewa koda a kai ga saka hannu a ido da hakan zai iya sa a saka kwayar cuta a cikin idon.

● A maida hankali matuka kan irin kayan da za a saka, wasu kayan za a iya goge su kai tsaye, wasu kuma ba haka ba. Idan za a cire kayan da aka saka lokacin da aka fita aiki, a tabbata an cire su cikin natsuwa da kula matuka. Sannan a wanke kayan da ruwa zafi da kuma sabulu sosai.

● Idan zai yiwu kada a rika mu’amula da kudi a lokacin da ake aikin dauko labarai. Sannan a rika goge katin ciro kudi wato ATM, da jakar ajiyar kudi a aljihu a kai-akai. Kuma ma a daina yawan saka hannu a aljihu.

● A kiyaye yin tafiya cikin motocin haya da kuma lokuttan da mutane ke sauri-saurin zuwa wuraren aiki da harkokin yau da kullum. Sannan kuma ka tabbata kana tafe da man tsaftace hannu tare da kai.

● Idan kuma a motar ka kake, ka kula sosai kada wani mai dauke da kwayoyin cutar ya shafa wa wani dake cikin motar, kamar yadda BBC ta ruwaito ya faru a kasar india,  a sassauke tagogi domin iska ya rika shiga yana fita sannan kuma inda hali ma a yi amfani da takunkumin fuska.

● A rika daukan hutu lokaci-lokaci, domin idan aka gaji da yawa za a rika yawan yin kuskure da mantuwa game da kiyaye kiwon lafiya. Saboda a dalilin yanayin irin aikin da ake yi  mutane za su yi dogon tafiya wajen zuwa da dawowa daga wuraren ayyukan su.

● Ka tabbata ka wanke hannayen ka sosai da ruwan dumi da sabulu a lokacin da za a fice daga inda cutar ta yadu.

● Idan ka ji rashin lafiya a jikinka kamar zazzabi ko yankewar numfashi, ka gaggauta ganin likita. Gwamnatocin kasashen duniya sun amince da a killace kai tukunna domin kada a yada cutar. Idan kana aiki a wuraren da annobar ta yi tsanani akwai yiwuwar za ka iya kamuwa da cutar, saboda haka a kula.

● A rika cin dafaffen nama da dafaffen kwai a koda yaushe.

Tsaftace Kayan Aiki

A kwai tabbacin cewa za a iya yada cutar COVID-19 ta hanyar kayan aikin da aka gurbata su da kwayoyin cuta. Dole a maida hankali wajen tsaftace su yadda ya kamata domin gudun kada a kamu da cutar kamar haka:

● A rika amfani da na’aurar daukar sauti mai tsawo wanda za a zuro shi daga can nesa.  Sannan kuma idan har za a yi amfani da na’urar daukan sauti wanda sai dole an makala a jikin mutum, a tabbata an bi dokokin samun kariya da kiyaye wa daga kamuwa da kwayoyin cuta.

● A rika rufe na’urar daukan sauti da rigarta sannan a goge da sinadarin kashe cuta idan aka gama aiki. A nemi sani da karin bayani game da yadda ake cire rigar na’urar domin kada a yada cuta.

● A yi amfanin da na’urar sauraren sauti da ake saka wa a kunne masu sauki. Wadanda idan aka gama amfani da su za a iya rabuwa da su. Amma wadanda za a ci gaba da amfani dasu a tabbata an tsaftace su da kyau bayan an kammala aiki.

● Ayi amfani da na’urar daukan hoto daga can nesa maimakon wanda yake dauka daga kusa. Hakan zai sa ayi nesa da wurin da ake fargaban kusanta domin kare kai.

● Idan zai yiwu ayi amfani kayan aikin tafi da gidan ka, ba wadanda sai anyi amfani da igiyoyin ko jone-jone ba.

● A kula da yadda za a adana kayan aiki. Kada a jibge su a  kasa. A maida su cikin akwatunan kayan aiki da jakkuna. Yana da kyau a yi amfani da akwatuna masu nagarta wadanda za a iya gogesu da man kasha kwayoyin cuta, a tsaftacesu bayan aiki.

● Idan zai yiwu a rika nade kayan aiki da murfin roba. Hakan zai rage sa kaya su kwashi kwayoyin cuta ko su gurbata da kwayoyin cuta. Kuma idan an gama aiki za a iya goge su da kyau ya fita.

● A tanadi batir din aiki guda biyu. Saboda a wajen kokarin cajin daya zai iya gurbata shi da kwayoyin cutar da za su iya shiga jikin mutum.

● A gaggauta goggoge kayan aiki da zaran an kammala aiki da sinadarin kashe kwayoyin cuta kamar Meliseptol, sannan a tabbata an goge da tsaftace wayoyin hannu, wayoyin wuta da kayan aiki, na’urar daukan hoto, da na bidiyo wato kamarori, Komfutoci da ababen adana da sauran su.

● Sannan kuma kafin a maida su wuraren da ake ajiyar su, a goggoge su, kuma a sanar wa masu kula da ajiyan wadannan kaya da kula da su a wuraren ajiyan domin  sun san yadda za su rika kula da kayan aiki da tsaftace su. A tabbata ba a ajiya kayan aiki barkate ba tare da an shigar su cikin jadawalin kayan da aka dawo da su ba sannan a tabbata ana kula da tsaftace su.

● Idan baka da sinadarin tsaftace kayan aiki. Ka sani cewa zaka iya baza su a rana na dan wani lokaci. Hakan na kashe cuta da ya manne a jikin kayan aiki. Za  ayi hakanne idan babu yadda za ayi domin yin hakan zai iya illata wasu kayan aikin.

● Idan za a yi amfani da mota ne a tabbata an tsaftace cikin motan da kyau musamman bayan an dawo daga wurin aiki. A samu wadanda suka kware wajen yin irin wannan aiki a basu su yi, za a goge  hannun kofofin mota, sitiyari, maduban hangen baya, radiyo, bel din kujeru, saman cikin mota da duk wani abu makamancin haka.

Tsaftace Na’urorin Dake Amfani Da Wutan Lantarki

A nan zamu bada shawarwarin da ya kamata abi wajen tsaftace kayan aiki da suka shafi wutan lantarki. Na farko dai ka tabbata ka karanta takardar da ke kunshe da na’urar wanda da ya zo da shi a kwali tun daga kamfani.

● Ka tabbata ka cire duk wani yawa dake makale da wurin wuta daga na’urar ka.

● A kauda duk wani abu na ruwa kusa da kayan aiki, wato na’urar ka. Kamar su man tsaftace wuri. Barin su su taba wannan kayan aiki zai iya lalata su.

● Kada ka fesa koma maenene akan na’urar ka

● Ayi amfani da kyalle masu laushi sannan masu tsafta wajen tsaftace kayan ka.

● Adan yayyafa wa wannan kyalle  ruwa amma ba a jika shi ba sannan a goga masa sabulu kadan.

● Daga nan sai a rika goge shi daga sama har kasa ana yi ana dawowa har ya fita.

● A kula kada ruwa ya shika cikin wuraren da ke bude a, kamar soket na wuta, da wuri tafin na komfuta da na’urar sauraren Magana wato Earphone. 

● A goge na’urori da kyallen da yake a bushe bayan haka.

● Wasu daga cikin kamfanonin kere-kere kan so ayi amfani da kyallen da ke dauke da akalla kashi 70% na sinadarin Isopropyl.

● Idan kana so ka tsaftace kayan aikin ka wato na’urorin ka, ka nemi bayanai daga kamfanin da suka yi wadannan na’urori domin akan samu matsala idan ba a fara bi daga wurin su ba anga irin sharuddan da suka saka akai ba.

Za a iya samun karin bayani a nan  

Kayan Sakawa Na Kare Kai Domin Kiyaye Kiwon Lafiya (PPE)

A nan ana nufin abubuwan da idan aka yi amfani da su za a jefar da su bayan haka, kamar safar hannu, takunkumin fuska, safa da takalman aiki. Wadannan kayan na bukatar a maida hankali matuka wajen kula da tsaftar su da yadda za a tsaftace su domin za su iya zama hadari idan ba ayi taka tsantsan ba. Dole sai an maida hankali. Za a samu cikakken bayani game da samun kula da kariya a shafin CDC a yanar gizo.

Akwai yiwuwar a gurbata kayan da za a yi amfani da su da kwayoyin cuta ta hanyar sakawa da cire kayan, za a iya yaduwa da cutar. Idan baka gamsu ba ka nemi kwararru su yi maka bayani, kafin a fita zuwa aiki.

A sani cewa a kasashe da dama, ire-iren wadannan kayan sakawa na kare kai kan yi karanci sosai saboda haka amfani dasu kan iya sa ayi fama da karancin su.

● A saka kaya kare jiki da yayi daidai da jiki. Saboda wanda ya yi kadan kan iya yagewa, idan kuma ya yayi yawa zai iya yana jan kasa ko kuma kama hannayen kofa su yage a lokacin da ake cikin aiki.

● Ayi amfani da kayan sakawa na kare jiki masu nagarta da aminci. A kula da kayan da basu da aminci kamar yadda Jaridar New York Times ta Wallafa da kuma irin wadanda basu da kargo kuma aka yi umarni kada ayi amfani da su kamar yadda ma’aikatun sarrafa kayan tsaro suka fadi. A bi nan domin samun kaya masu aminci da  nagarta 

● A saka safar hannu lokacin aiki ko kuma a lokacin da aka ziyarci mara lafiya. Idan so samu ne ma a sake guda biyu a hannu. 

● Idan za a yi aiki a wuraren da annobar ta yi tsanani yana da matukar mahimmanci a tafi da karin kayan sawa kamar rigar kariya da takunkumin fuska da safar hannu da dai sauran kayan kare jiki da za a bukata.

● Idan za a saka kayan kariya duk jiki ne a tabbata an yi amfani da ban daki kafin a saka saboda kaucewa lalurar haka zai iya tasowa.

● Sannan kuma yana da matukar mahimmanci a samu kwararre ya  adana kayan aiki na kariya da za a fita da su domin ko anan ma akan iya gurbata su da kwayoyin cuta.

● Ma’aikaci na bukatar saka takaman da ruwa baya ratsa su ko kuma takalman aiki da ake rabuwa da su bayan an yi amfani da su. Sannan kuma a tabbata an wanke su tsaf bayan an gama amfani da su kafin a bar wurin aiki. Idan na yar wa ne a tabbata an jefar da su yadda ya kamata kafin a bar wurin.

● A tabbata an saka kuma an cire kayan kariya  a karkashin kulawar kwararru.    Saboda zai iya yiwuwa wannan lokaci ne za su iya kwasar kwayoyin cuta.  Wannan bidiyo game da yadda za a saka da cire kaya daga CDC zai taimaka matuka  sai dai kada a dogara da shi aki zuwa a koyi yadda ake saka kayan da cirewa kamar yadda kwararru suka koyar.

● Ka da a kuskura a yi amfani da safar hannu wanda saudaya yakamata a yi amfani da su sau biyu, ko kuma rigar aiki dake rufe jiki ko takalman aiki. Idan akwai abin da za a iya sake amfani dasu, tabbas sai kwararru sun tsaftace su da sinadarin kashe kwayoyin cuta. Sannan ka tabbata an jefar da duk wani abinda ba za a sake amfani da shi ba kafin a bar wurin.

Takunkumin Fuska

Ana samun karin kasashen dake tilasta wa mutane saka takunkumin fuska kamar yadda Aljazeera ta ruwaito. CDC ta bada shawarar a rika saka takunkumin fuska da aka yi su da kyalle maimakon na ainihi, saboda ana karancin su matuka, domin amfani dasu wajen rufe hanci da baki. Hukumar WHO ta yi gargadi cewa wadanda suka sheka 60 a duniya da kuma wadanda ke fama da rashin lafiya mai tsanani su rika saka takunkumin ainihi wato wanda lilkitoci suka amince da irin su, musamman idan ba za su iya yin nesa-nesa da mutane ba.

Saka takunkumin fuska yadda ya kamata na da matukar amfani musamman ga ‘yan jaridan da suke aikin ci gaba da dauko labarai  a wuraren su, da ya hada da dole sai an tafi wasu kebabbun wurare, ko kuma wuraren da akwai dandazon jama’a kuma su yi hira ko dauko labarai a irin wadannan wurare. A ranar 9 ga Yuli, hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewa akwai yiwuwar za a iya kamuwa da kwayoyin cutar COVID-19 ta hanyar shakar iska a wasu yanayi na musamman. Irin wadannan wurare sun hada da wuraren da aka kebe, wato kamar kananan dakunan da babu iska dake shiga ya fita da kuma wuraren da akwai cunkoson mutane. Ka sani cewa za a samu yaduwar kwayoyin cuta irin haka a wurare irin nan wanda zai saka cikin hadari matuka.

Sai dai fa a tabbata an saka takunkumin da kyau gaske domin rashin haka na zama sanadiyyar kamuwa da cutar

A wani rahoton binciken Lancet, kwayoyin cutar kan iya zama a jikin takunkumin har na tsawon kwanaki bakwai bayan anyi amfani da shi, ko kuma taba fuska a lokacin da aka saka shi kan zama hadari ga mutum.

A dalilin haka, cire takunkumin, ko kuma amfani da wanda akayi amfani dashi a baya zai iya zama hadari.

Idan za a saka takunkumin fuska a tabbata an bi wadannan ka’idoji dake tafe:

● Abin da yafi dacewa shine a sake takunkumi fuska kirar N95 ko kuma  (FFP2/FFP3) maimakon wanda likitoci ke sakawa idan za suyi aikin fida a asibiti.

● Sannan kuma a tabbata ya rufe ko-ina a fuska tun daga hanci da gefen kumatu, kuma a tottoshe kafofin gefen kumatu. A aske duka gashin fuska ko kuma a rage shi matuka saboda takunkumin ya zauna da kyau a fuskar mutum ba tare da an samu wani kafa da kwayar cutar za shiga baki ko hancin mutum ba.

● Kada a rika taba shi wannan takunkumi idan aka saka kuma ida za a cire ayi amfani da igiyan sabulewa. Kada a kuskura a taba fuskar takunkumin. A gaggauta wanke hannu idan aka taba takunkumin.

● A rika wanke hannu a koda yaushe da ruwan dumi da sabulu ko kuma da man tsaftace hannaye dake kasha kwayoyin cuta mai kunshe da sinadarin ethanol akalla kashi 60% ko 70% na isopropanol bayan an cire takunkumin fuska.

● A gaggauta canja takunkumin fuska da wani idan ya dade a jiki da sabo kuma mai tsafta.

● Kada a sake amfani da takunkumin da aka yi mafani dashi a baya, sannan idan za a jefar a saka shi cikin rufaffen jakar tara bola.

● A tuna cewa shi saka takunkumin fuska daya daga cikin hanyoyin kare kai ne, dole sai ana kuma wanke hannaye da ruwan dumi da sabulu sannan a daina taba fuska da ya hada da idanu, baki, kunnuwa da hanci.

● Auduga da takunkumin kyalle basu inganta a yi amfani da su ba kwata-kwata.

● Wani abu kuma da ya kamata ka sani shine shi takunkumin fuska kan iya yin karanci ko kuma su yi tsadar gaske, sai dai ya danganta ne da inda kake aiki.

Tsaro Daga Muzantawa Daga Yanar Gizo

● Dole ne ‘yan jarida su kwana da shirin cewa za a rika cakalar su da muzanta musu kan labarai da rahotannin da za su rika yi kan annobar cutar COVID-19. Ka bi shafin CPJ domin samun bayanan  yadda za ka kare kan ka, da kuma tsayawa tsayin daka daga fadawa hannun masu kawo hari ko muzantaka.

● Gwamnatoci da kamfanonin fasaha na kirkiro hanyoyin bin diddigin yadda cutar COVID-19 ke yaduwa a duniya. Kamfanin NSO Group da ta kirkiro da Pegasus manhaja ko na’urar da ake iya bin diddigin ‘yan jarida da halin da suke ciki idan aka afka musu  tsangwama ko makamancin haka. Kamar yadda Citizen Lab ya bayyana. Kungiyoyin rajin kare hakkin mutane sun afka cikin fargaba da nazarin yadda za ayi amfani da wannan fasaha ko na’ura wajen bin diddigin ayyukan ‘yan jarida. Haka ita ma kungiyar bin diddigi ta (Transparency International) na bibiyar ayyuka irin wadannan miyagu a shafinta dake yanar gizo.

● Ka dan dakata ka yi nazari kafin ka latsa wani shafi a yanar gizo don samun labaran COVID-19. A kwai miyagu da suke amfani da wannan annoba da ta karade duniya wajen yada muggan fasaha da suka kirkiro da zai rika nuna musu halin da kake ciki da kuma samar musu da bayanan ka, kamar yadda Electronic Frontier Foundation ta wallafa. Saboda haka a kula matuka.

● Kuma ka yi taka tsantsan da irin shafukan da zaka rika bi a yanar gizo wajen nemu ko samun bayanai kan cutar COVID-19, ko kuma wasu manhajojin da za su iya illata maka na’ura sannan su rika bada bayanan ka na sirri a boye.

● A kula kuma da wasu manhajoji da fasaha da aka kirkire su a yanar gizo domin damfara da ake amfani dasu a wannan lokaci da kowa yake so ya san me ke faruwa game da cutar kamar fasahar da aka kirkiro mai suna COVID-19 Tracker.

● Haka kuma taswirorin dake nuna bayanan yaduwar cutar COVID-19 wadanda ma aka yarda da su kamar na WHO an samu rahoton cewa suma na daukar irin wadannan muggan fasaha dake zakulo bayanan mutum na sirri.

● A yi takatsantsan da rahotannin karya da wasu hukumomin gwamnati ke biya a saka kamar yadda aka ruwaito a jaridar The Guardian, da kuma rahotannin da basu tabbata ba kamar yadda hukumar WHO ta yi gargadi game da haka kuma BBC ita ma ta fitar da bayanai kan haka. Akwai wani kundin bayanai game da haka mai suna A Myth buster guide a shafin WHO.

● A maida hankali matuka game da manhajojin  da kake amfani dasu wajen tura sakonni, da yawa daga cikin su na dauke da labaran karerayi ne kawai da fasahar satar bayanan ka.

● Sannan kuma ka sani cewa duk bayanan dake kunshe da rahotonin COVID-19 da ke shafin Facebook  ana yi musu binciken kwa-kwaf ta hanyar amfani da dabarun bincike da  kimiyya da sarafa bayanai na zamani wato (AI) maimakon dan Adam, da a dalilin hakan ya sa  a kan iya samun sahihan bayanai da aka goge cikin kuskure.

● Ka yi bincike da nazarin sanin tsaro na yanar gizo sannan ka san wani shafi kake ziyarta kuma ka ke tura sako da samun bayanai, sannan kuma da sanin matsayin tsaron shafin kafin ka yi hulda da su. Domin mutane da dama suna zaman gida dole, hakan zai ba masu satar bayanai damar cin karen su ba babbaka.

● A yi takatsantsan wajen dauko labarai daga  kasashen da gwamnatocin su ke da tsauri wato gwamnatin kama karya wanda za ta rika bibiyar yadda ake dauko wa da yada labarai game da annobar cutar COVID-19. Wasu gwamnatocin  za su so su boye ainihin bayanai game da cutar ko kuma sai sun tantance gidajen jaridun da za su rika dauko labarai a kasashen su kamar yadda CPJ ta bayyana a shafinta.

Laifuka da Tsaron Kai A Lokacin Aiki

‘Yan jarida su kwana da shirin cewa za a rika tsangwamar su ta hanyar afka musu kai tsaye ko kuma ta hanyar jifar su da kalamai batanci  a lokacin da suka aiki kamar yadda aka gani a kasar Amurka, kamar yadda yake kunshe a rahotan cibiyar bin diddigin ‘yancin ‘yan jarida ta kasar Amurka, Jamus, UK, Indiya da Somalia.

Tallalin arzikin kasashen duniya na ci gaba da yin barazanar tabarbarewa, ganin yadda mutane ke ci gaba da ra sa ayyukan su da kuma yadda akalla sama da rabin mutum biliyan 1 suka fada cikin tsananin talauci kamar yadda Oxfam ta bayyana za a rika samun ayyukan batagari na kara yawa.

Lallai akwai tabbacin za a rika samun yawa-yawan masu aikata laifuka musamman laifuka ta yanar gizo kamar yadda rahotan bayanan binciken da jami’ar Cambridge tayi

● Idan har za ka yi tafiya aiki kasashen waje ka duba nan. Ka tabbata ka yi bincike mai zurfi kan inda zaka tafi aiki. Duk da cewa an samu raguwar tashin tashina da ake samu a dalilin garkame mutane da aka yi, an samu rahotan zanga-zangar masu tsanani a kasashe da dama tun daga watan Fabrairu. Ka kwana da shirin cewa akwai yiwuwar sake barkewar ire-iren wadannan zanga-zanga idan cutar ta sake barkewa a karo ta biyu kuma aka sake kulle mutane.

● Da yawa daga cikin manyan birane zaka ji sun yi shiru tsit ba kamar da ba, wanda hakan yasa za a samu karancin ‘yan sanda. Miyagun mutane za su iya amfani da wannan dama su rika aikata ta’addanci. Wasu ‘yan jarida da dama sun yi kukan fadawa hannun ire-iren wadannan mutane, wasu an ci zarafinsu wasu an muzguna musu wasu kuma an rika kai musu hari. Saboda haka kada koda wasa kayi sakwa-sakwa da tsaro da lafiyar ka.

●  ‘Yan jarida su kiyaye matuka idan aiki ya kai su kauyuka ko karkara, domin wasu basu saba da baki ba, kuma za su iya yi maka ganin ka shigo musu gari da cutar COVID-19.

● A kuma maida hankali wajen kiyayewa da fushin ‘yan sanda lokacin aiki musamman a yanayin da aka garkame gari don COVID-19, kamar cin zarafin mutane, sannan sukan yi amfani da harsashen gaske,  barkonon tsohuwa, da harsashen roba.

● Idan mutum yana aiki a gidajen kaso ko kuma inda a ke tsare masu laifi, dole dan jarida ya yi takatsantsan sannan ya maida hankali da irin hadarin da zai iya bijirowa a dalilin ko yin zanga-zangar wadanda suke tsare a dalilin cutar COVID-19, kamar yadda aka gani a kasashen Sierra Leone Italiya, Najeriya, Columbiya da Indiya.

● Dan jarida ya kiyaye matuka domin akwai yiwuwar kara samun tashin hankali da aikata laifuka a wannan yanayi ganin yadda kasashe kamar su Iraq, Amurka, Ireland, Indonesia , Ethipia, Palastine, Somalia da Iran sun saki fursinoni da ke garkame a gidajen kason kasashen saboda a rage cunkoso a dalilin annobar COVID-19.

 ● A maida hankali matuka dan ayyukan  ta’addanci da kwace da ya hada da sace-sace  da fashi musamman idan aka sake saka  dokar hana walwala a wasu kasashen ko kuma idan rasa aiki yayi wa mutane yawa. 

● Lallai dole dan jaridan dake aiki a kasashen da ake mulkin kama-karya ya zamo cewa a kullum yana zaune ne cikin shirin yi masa barazanar ko a kama shi a daure ko a cafke shi a lokacin da yake aikin dauko labaran cutar COVID-19 kamar yadda CPJ ta bayyana.

Aikin Dauko Labarai Daga kasashen Waje

A dalilin dokar hana tafiye-tafiye da kasashen duniya suka saka, yanzu tafiya zuwa wata kasa baya samuwa cikin sauki kamar a baya. Idan har tafiya zuwa wata kasa ya kama ka, ga matakan da zaka bi:

● Ka kula matuka cewa dokar hana zirga-zirga kan banbanta daga kasa zuwa wata kasa. Kuma za a ci gaba da samun irin wadannan canje-canje ba tare da mahukunta sun yi sanarwa akan haka ba. Kwatsam sai dai mutum yaci kwai an zartas da wata doka kuma har ta fara aiki.

Za a iya killace ka ba tare da an sanar maka da haka ba da zaran ka dawo daga aikin dauko labarai. Hakan kuma ya danganta musamman da kasar da ka dawo aiki daga. Kamar yadda aka gani daga mutanen da suka dawo kasar Birtaniya wato United Kingdom daga kasar Spain.

● Ka nemi sanin matsayin kiwon lafiya a kasashen da zaka je aiki. Ma’aikatan kiwon lafiya za su iya yin bore a kowani lokaci ba tare da sun sanar ba  kamar yadda muka gani a kasashe kamar su Indiya, Sierra Leone, Nigeria da Kasar Faransa

● Samun kayan kariya zai iya yin karanci ko kuma a rasa su kwata-kwata. Ka tabbata ka yi bincike mai zurfi game da yadda zaka mallaki naka ko kuma mafi sauki ka tanadi naka kafin ka fita zuwa aiki.

● Ka tabbata duka rigakafin cututtukan da ya kamata ayi su a kasar an yi su akan lokaci sannan kaima ka yi allurar rigakafin cutar mura saboda kada alamun haka ya kawo cikas ko rudani.

● Ka duba dokokin Inshorar tafiyar ka. Ganin cewa samun wata takarda da zai wanke ka daga cutar COVID-19 zai yi wuyan gaske. Ka sani cewa gwamnatocin kasashe kan bada shawarwari game da tafiye-tafiye da gargadi game da tafiya zuwa  kasashen duniya. 

● Ka rika duba bayanai game da taron da zaka halarta, saboda kasashe da dama sun hana taron mutane ko kuma taron da ya wuce wani kayyadadden adadin mutane.

● Ka yi binciken sabbin dokoki game da shige da ficen kasashen inda zaka domin akan samu canji kwatsam ba tare da an sanar da haka ba.

● Ya kuma kamata ka yi tafiya cikin shiri, domin wasu manyan garuruwan, yankuna da kasashen gaba daya duk za a iya garkame su ba tare da an sanar ba kwatsam sai a saka dokar. 

● An daddatse iyakokin kasashe a fadin duniya. Wadanda aka bude ma za a iya dates su kuma, saboda haka ya kamata ka tsara irin haka cikin shirin ka na ko ta kwana.

● Kada ka kuskura ka yi tafiya idan baka da lafiya. Kusan duka tashoshin jiragen saman kasashen duniya sun saka tsauraran matakan gwajin lafiyar matafiya. Za a yi wa matafiya gwaji a filayen jiragen saman, wasu ma sai an killace su, ko kuma ka killace kanka lokacin daka isa wannan filin jirgi.

● Har yanzu akwai matsalolin dama na tafiye-tafiye da yayi tsanani saboda yadda jirage ke soke tashi da sauka a kasashe. 

● Ka sayi tikitinka na Jeka ka dawo, ka siya tikitin da idan ma bai yiwuba ra a biya kudin ka. Annaobar COVID-19 ya sa kamfanonin jiragen sama sun fada cikin matsalar karancin kudi. Kamar yadda rahotanni suka nuna.

● Ka tabbata ka tanadi duk abin da zaka bukata a inda zaka je duk da dai yanzu ba a samun mutane suna rigerigen siyayya  , duk da haka za a iya samun karancin  sinadarin tsaftace hannu, Sabulai, abincin gwangwani, takunkumin fuska da dai sauransu. Sannan kuma ka sani a dalili ko rashin ma’aikata na yajin aiki ko kuma an rufe wuraren da za a iya siya saboda annobar COVID-19 a inda zaka  yi aiki zai iya sa abin yayi wuya.

● Ka duba matsayi ko hanyar samun bizar kasar da zaka je domin kasashe da dama sun dakatar da bada biza kuma wadanda suka bada a baya ma duk sun soke su.

● Ka tabbata ka duba matsayin kasar da zaka je game da shaidar lafiyar ka, ko kila sai ka nuna shaidar baka dauke da cutar COVID-19 kafin a baka damar shiga kasar. 

● Ka tabbata ka samu isasshen lokaci a tashoshin jirgen sama domin gwaje-gwaje da za a rika yi da ya hada da na lafiyar ka da na gwajin zafin jikin ka  a wurare a filin jirgin. Haka kuma ma a tashoshin jiragen kasa, ruwa da tashoshin shiga manyan motocin haya.

● Ka tabbata kana sane da kuma bibiyan canje-canje da ka iya samuwa a daidai lokacin isarka kasar da zaka je. Wasu kasashen kan sa baki su sauka a wani bangare ne na tashar ko kuma ma wani filin jirigin dabam.

● Ka maida hankali wajen sauraren labaran kasashen da zaka ziyarta ko kuma ka ke aiki a ciki domin sanin canje-canje da sabbin dokoki da aka saka game da walwalar jama’a a wannan kasa.

Bayan An Kammala Aiki

● Ka rika duba lafiyar ka akai akai domin gano ko akwai alamun kamuwa da wata cuta

● A dalilin aikin da ka yi bayan kadawo zai iya yiwuwa dole sai ka killace kanka musamman idan ka dawo daga kasar da annobar ta yi tsananin gaske. Ka duba yadda dokokin kasar ka suke domin fahimtar yadda za aka tunkari abin.

● A maida hankali wajen sani da sa ido kan sabbin dokoki ko matakai da bayanai da da za a rika fitar wa game da cutra COVID -19, da kuma bayanai game da killace kai da garkame mutum a kasar ka ta asali da kuma kasar da tafi aiki. 

● Yana da matukar mahimmanci ka mallaki jadawalin sunayen wuraren da ka ziyarta, sunaye da yawan mutanen da ka yi mu’amula da su a tsakanin kwanaki 14 bayan ka dawo daga tafiya. Hakan zai taimaka matuka idan ana neman wadanda ka yi mua’amula da su a lokacin da aka fara ganin alamun rashin lafiya a jikin ka.

—Idan Ka Nuna Alamun Rashin Lafiya

● Idan ka fara jin alamun rashin lafiya irin ta COVID-19 komai kankantarshi Ka nemi shugabannin ma’aikatarka su san halin da kake ciki domin su nema maka motar da zai kai ka gida maimakon ka yi gaban kanka ka fada motar haya kawai ka yi tafiyar ka.

● Ka tabbata ka bi shawarwarin da hukumar lafiya ta duniya, WHO, CDC da ma’aikatar kiwon lafiya suke bayarwa domin kare kanka da na al’umma gaba daya.

● Kada ka fita daga gidan ka na tsawon kwanaki 7 daga lokacin da ka fara jin alamun rashin lafiya. ( Koda yaka ainihin lokacin da za ka iya fita ko yin mu’amula ya danganta da yadda gwamnatin kasar ka ta tsara ne bias shawarwarin da za a baka.) Yin haka zai taimaka wajen kare al’umman da kuke zaune tare a lokacin da ka kamu da kwayoyin cutar.

● Ka tsara wa kanka yadda zaka yi zama a killace. Ka nemi taimakon wadanda kuke tare. Abokanan aikan ne, abokai da ‘yan uwanka su taimaka maka da abubuwan da kake bukata, su ajiye maka a kofar dakin da kake. Daga baya kai ka fito ka dauka

● Ka tabbata ka bi dokokin yin nesa da mutane kamar yadda mahukuntan kasarka suka ayyana ko tsara. 

● Idan so samu ne, ka kwana kai kadai a daki shi ya fi.

● Idan kana kwana daki daya da wasu ne, A samu wani tsawon lokaci da za killace kai na da matukar mahimmanci.  Za a iya samun bayanai masu amfani game da haka a nan. A kuma kiyaye wajen amfani da dakin wanka, dakin bahaya da dakin girki, musamman wajen amfani da cokula da kayan girki saboda a kauce wa kamuwa cuta. 

● Ka wanke hannayen ka da ruwan dumi da sabulu na akalla sakan 20 a koda yaushe.

● Ka ni santa kan ka daga mutane masu rauni, kamar gajiyayyu da marasa lafiya a koda yaushe.

● Ba sai ka nemi taimakon ma’aikatan kiwon lafiya kasar kaba idan zaka killace kanka, sai dai idan alamun rashin lafiyan ya yi tsanani a lokacin da ke killace.

Kwamitin Kare ‘Yan jarida CPJ ya samar wa ‘Yan jarida da dakunan ‘yada labarai muhimman bayanai kan yadda za su rika kiyaye kansu a duk halin da suka tsinci kansu na aiki, kai tsaye ne, ta yanar gizo ne da kuma yadda zaka inganta tunanin ka da kauce wa fadawa cikin fargaba da rudani da fadawa cikin damuwa da yadda za a kiyaye, har a lokacin da ka tsinci kanka wajen  dauko labarai lokuttan rashin zaman lafiya  da lokuttan zabe.

 [ Sakon Mawallafi:  An wallafa wannan shawarwari a karon farko  ranar 10 ga watan Fabrairu, 2010, sannan kuma ana ingantashi akai-akai da sabbin bayanai. Ranar da aka saka a saman wannan rubutu, shine sabon bugu da aka yi na karshe.]